Daga Rukayya Abdullahi Maida
Yayin da al’ummar jihar Kogi ke shirin gabatar da zaɓen gwamnan jihar a ranar 11 ga watan Nuwamba, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya ce yana sa ran kashi 99 cikin 100 na goyon bayansu don samun nasara jam’iyyar a jihar.
Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar APC da magoya bayanta a wajen kaddamar da kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar a zaɓen ranar 11 ga watan Nuwamba.

Ya bayyana fatan al’ummar jihar za su kada kuri’arsu ga jam’iyya mai mulki domin jihar kogi dama jiha ce ta APC tuntuni, inji rahoton NAN.
Tinubu ya umarci jakadun Nigeria dukkanin su su koma Gida
“A yau muna kaddamar da kwamitin yakin neman zabe na jiha a hukumance wanda zai hada hannu da kwamitin yakin neman zabe na kasa da kuma kwamitocin yakin neman zabe na kananan hukumomi domin ganin mun sami nasara a zaben dake tafe”. Ganduje
“Kun ga irin kyakkyawan shugabancin da gwamnatin Gwamna Yahaya Bello ta yi muku, don haka a matsayinmu na jam’iyyar muke fatan za ku kara bamu dama don zabar dan takarar mu, Usman Ododo, domin yi muku aiyukan alkhairi .

Ododo danku ne, wanda kuka sani sosai a matsayin mutumin kirki mai aminci da aiki tukuru wanda a shirye yake hidimta muku da jihar kogi baki daya idan ya zama gwamna.
Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya Nada Karin Manyan Mataimaka 57
“Ba mu sa ran samun nasara kasa da kashi 99 cikin 100 daga mutanen Kogi a zaben gwamnan da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba,” in ji shi.
Ya shaida wa mazauna jihar cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin samar da kyakyawan yanayin da ake bukata domin gudanar da zaben gwamna cikin lumana da aminci.