Daga Sani Idris Maiwaya
Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya amince da sake nada sabbin masu bashi shawara na musamman guda 14.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24.
Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya Nada Karin Manyan Mataimaka 57
Sanarwar ta ce idan ba’a manta ba majalisar dokokin jihar kano a kwanakin baya ta amincewa gwamnan ya nada masu bashi shawara na musamman har guda 60 , kuma tuni ya nada 31 daga cikin su .
Ga jerin sunayen wadanda aka nada din:
1. Dr. Danyaro Ali Yakasai, Special Adviser, Policy and Social Development
2. Alh. Garba Aliyu Hungu, Special Adviser, Industries

3. Dr. Bashir Abdu Muzakkari Fagge, Special Adviser, Cyber Security
4. Hon. Ismail Shehu Gurjiya, Special Adviser, Grassroot Mobilisation
5. Hon. Nasiru Kunya, Special Adviser, Support Groups
6. Hon. Ali Yahuza Gano, Special Adviser, Metropolitan Affairs
7. Hajiya Habiba Mustapha Baura, Special Adviser, Domestic Affairs
8. Hajiya (Dr.) Fatima Abubakar Amneef, Special Adviser, Special Assignment (Women)
9. Hon. Yusuf Shehu Kibiya, Special Adviser, Community Policy
10. Hon. Ali Abdu Doguwa, Special Adviser, Political Strategy
11. Hajiya Aisha Muhammad Idris, Special Adviser Food Security
12. Hon. Shehu Aliyu Yammedi, Special Adviser, Lafiya Jari Programme
13. Comrade Nura Iro Ma’aji, Special Adviser, Students Matters
14. Dr. Abdulhadi Zubairu Chula, Special Adviser Enlightenment and Social Mobilisation
Sanarwar ta bukaci sabbin mashawarta gwamnan da su gaggauta zuwa inda aka tura su domin fara aikin da aka dora musu.