Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Kungiyar bunkasa gasa ta kasa da kasa ta Africa mai suna Pan African Competitiveness Forum ta zabi Dr. Abubakar Tanko Bala hamshakin kasuwar nan a matsayin Sakatare janar kungiyar reshen Nigeria .
Dr. Abubakar Tanko Bala hamshakin dan kasuwa ne kuma mashawarci kan harkokin kasuwanci, haka zalika shi ne Ma’ajin Kungiyar Kananan Masana’antu ta Nigeria (NASSI).

A wata sanarwa da Kakakin ofishin babban Sakataren dake Nigeria Fa’iza Shehu ta aikowa kadaura24, tace a ranar Juma’a 1 ga watan Satumbar, shekara ta 2023, Dr. Abubakar Tanko ya zama babban sakataren kungiyar Pan African Competitiveness Forum (PACF) wanda aka gudanar da bikin a Sheraton Hotel Abuja.
Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya Nada Karin Manyan Mataimaka 57
Ita dai kungiyar Pan African Competitiveness Forum wato PACF an ƙirƙire ta ne don haɓaka tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta hanyar samar da Ƙungiyoyin da za su inganta tare da haɓaka tsakanin waɗannan ƙasashe.
Alh Garba Ibrahim Gusau Mni, MFR, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar PACF tare da ma’ajin kungiyar na kasa Alhaji Abdul-Fatah Shittu sune suka jagoranci taron tare da rantsar da Dr. Abubakar Tanko Bala matsayin babban sakatare na kungiyar PACF.
Bikin wanda aka yi shi cikin nasara da kyakyawan fatan Dr. Abubakar zai taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da kungiyar PACF gaba a matsayinsa na Sakatare Janar sakamakon ya cancanci rike mukamin da aka zabe shi.
Kungiyar Pan African Competitiveness Forum dai ta na da karfi Sosai tana bada gudunmawa matuka wajen cigaban tattalin arzikin kasashen Africa, sanna kuma tana cikin kungiyar kasashen Africa wata AU, tana Kuma da alaka da kungiyoyin taimakawa al’umma na kasashen duniya sama da 72.