Daga Nasiru Abubakar
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ayyana Litinin, 1 ga Muharram, 1443 AH (9 ga Satumba, 2021) a matsayin Ranar hutun sabuwar Shekarar Musulunci a jihar.
Sanarwar da kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ya sanya wa hannu ta bayyana cewa hutun ya kasance ne don tunawa da sabuwar kalandar Musulunci ta 1443 AH.
Gwamnan ya bukaci ma’aikata da su yi amfani da ranar don yin addu’a ga jihar Kano da kasa don kubutar da ita daga matsalolin tsaro.
Gwamna Ganduje ya kuma taya Musulmai murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci, wacce ke bukatar nuna godiya ga Allah .
Sanarwar ta kara neman goyan baya da hadin kai na jama’a ga gwamnati yayin da take yin bakin kokarinta don inganta kudirinsu yayin da kasar ke fuskanta kalubalen tsaro.