Zargin kazafi: Hadimin Sanata Barau ya maka Wani Musbahu Gadar Lado a kotu

Date:

Daga Zainab Muhd Darmanawa

Babbar kotun Shari’a Musulunci dake Zamanta a hotoro a jihar Kano ta aike da sammaci ga Wani sojan baka Mai Suna Musbahu Ibrahim Gadar Lado kan kararsa da Mai Magana da yawun Sanata Barau Jibril Shitu Madaki Kunchi yayi bisa zarginsa da yiwa Sanata Barau kazafi.

Kadaura24 ta rawaito Cikin takardar sammacin Mai lamba 213/21 wadda kotun ta aikewa Wanda ake zargin, kutun ta Bukaci ya baiyana a gaban kotun a Ranar litinin 09/08/2021 domin Fara shari’ar.

Tun a Ranar 04 ga Wannan Wata da muke ciki ne ofishin lauyoyin na Tanimu Yahya & co Suka rubutawa Kwamishinan Yan Sanda na Jihar Kano korafi Kan Musbahu Ibrahim Gadar Lado a madadin Wanda suke karewa Shitu Madaki Kunchi.

Takardar korfin ta Zargi Musbahu Ibrahim Gadar Lado da yiwa Sanatan Kano ta Arewa Sanata Barau Jibril kazafi tare da ikirarin cewa Sanatan ne ya basu kudi domin su yiwa Mataimakin Gwamnan Kano da Uwar Gidan Gwamna ihu Yayin Wata Ziyarar aiki da suka Kai Karamar Hukumar Bichi.

Takardar ta bukaci kwamishinan Yan Sanda Daya bada dama a gudanar da Bincike Kan wancan Zargi da ake yiwa Musbahu Ibrahim Gadar Lado Wanda aka ce yayi ikirarin ne a Cikin Wani hoton Bidiyo Daya saki ya dandalin sada Zumunta.

42 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...