Daga Aisha Muhammad Adam
Al’ummar dake zaune a unguwar Danbare da kewaye dake karamar hukumar kumbotso a jihar kano sun Koka da mawuyacin halin da suke cikin sakamakon lalacewar hanyar su.
Wasu mazauna yankin da suka zanta a jaridar kadaura24 sun bayyana cewa suna kasancewa cikin damuwa duk lokacin da aka ce an yi ruwan sama.

” Marasa lafiya da dama sun rasa rayukansu wasu kuma sun kara jigata sakamakon lalacewar hanyar mu ta danbare, kuma ko masu adaidaita sahu ma basu son bin hanyar saboda lalacewar da ta yi, kin ga idan ba ka sami abun hawan da zai kai gida ba ai akwai matsala”. Inji Wani zaunin unguwar Danbare
Da dumi-dumi: Kotun daukaka kara ta yi watsai da bukatar Abba Kabir Yusuf
Mazauna yankin wadanda suka bukaci a sakaye sunansu saboda yanayin tsaro, sun ce ‘ya’yan su sukan makara idan zasu makaranta saboda lalacewar hanyar, haka suma magidanta su kan makara idan zasu wajen aiki.
” Muna bukatar gwamnatin jihar kano ta Kawo mana ɗauki domin fitar da mu daga cikin wannan mawuyacin halin na rashin hanya a unguwar mu ta danbare”.
Tinubu ya sake tura tawagar Malamai zuwa Jamhoriyyar Nijar
Jaridar kadaura24 ta yi kokarin jin ta bakin shugaban karamar hukumar Kumbotso Alhaji Hassan Garban kauye farawa domin jin shi wai yasan halin da al’ummar sa na unguwar Danbare suke cikin ? In ya sani wanne kokari yake yi domin magance matsalar da suke fuskanta? .
Sai dai duk kiran da muka yiwa shugaban karamar hukumar bai shiga ba, amma mun tura masa da sakon karta kwana, amma har lokacin haɗa wannan rahoto bai Magantu ba akan maganar za kuma u cigaba da bibiya.
Ga wasu daga cikin hotunan yanayin da titin yake ciki