Tinubu ya sake tura tawagar Malamai zuwa Jamhoriyyar Nijar

Date:

 

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sake tura tawagar malaman addinin Musulunci zuwa jamhuriyar Nijar domin sake tattaunawa da jagororin juyin mulkin ƙasar.

 

Makonni biyu da suka gabata ne malaman suka ziyarci Nijar, inda suka gana da shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Abdourahamane Tiani.

Talla

Tinubu ya yanke shawara sake aika tawagar malaman ne ranar Alhamis bayan ganawa da manyan malaman musuluncin ƙarƙashin jagorancin Sheikh Dahiru Bauchi.

http://KU KARANTA: Kotun daukaka kara ta yiwa watsi da bukatar Abba Kabir Yusuf

Shugaba Tinubu ya yanke shawarar ne a matsayinsa na shugaban ƙungiyar Ecowas.

Ecowas ta yi ta ƙaƙaba wa Nijar takunkumai tun bayan juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi ranar 26 ga watan Yuli.

Abubawan da muka tattauna da masu gabatar da Shirin Mata a Yau na Arewa24 – Sheikh Aminu Daurawa

A ƙarshen mako ne tawagar Ecowas ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Abdussalmi Abubakar mai ritaya, ta kai ziyara ƙasar a kokarin shiga tsakanin ƙungiyar da sojojin Nijar, inda ta samu ganawa da hamɓararen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum da shugaban mulkin sojin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sanarwa ta Musamman daga majalisar malaman Kano game da rasuwar Dantata

SANARWA MUHIMMIYA (GABATAR DA SALLATUL GA'IB) Assalamu Alaikum Warahmatullah, Sakamakon rasuwa...

Aminu Dantata ya bar mana wasiyyar inda za a binne shi – Iyalansa

Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Dantata sun shaida cewa...

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...

Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447AH

    Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala...