Gwamna Ganduje yace ya kadu sosai da mutuwar Col. Dominic Oneya

Date:

Daga Sa’eeda Ahmad Sagagi

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana kaduwarsa kan rasuwar tsohon Gwamnan Kano Zamani mulkin Sojoji, Kanal Dominic Obukadata Oneya, wanda ya rasu a yau, Alhamis.

Wannan na kunshe ne Cikin Wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran Gwamnan Kano Malam Abba Anwar ya aikowa Kadaura24.

“A lokacin da yake Gwamnan Kano na Soja , Kanal Dominic Oneya ya yi iyakar ƙoƙarinsa wajen ciyar da jihar gaba,” in ji Ganduje.

Ganduje yace Oneya Yana da hangen nesa wajen gane abun da al’umma suke bukata Wanda Zai Kawo cigaba a Lokacinsa.

” A matsayina na Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri a ƙarƙashinsa, na san yadda yake da kishin ƙasa. Da gaske mun rasa dan kasa mai kishin kasa, ”in ji gwamna Ganduje.

Gwamna Ganduje ya nemi iyalan Marigayin da su yi koyi da kyawawan halayen mahaifinsu. Wanda ya jajirce wajen cigaban kasa kuma jagora mai kishin kasa.

“Har yanzu Kano tana amfana daga ginshiƙan tushe na marigayin ya kafa wa jihar abubuwa masu kyau, waɗanda wasu gwamnatoci suka kwafa daga baya,” in ji shi.

Ya yi fatan Iyalan Mamacin za su sami karfin gwiwa don jure rashin.

74 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...