Yanzu-Yanzu: Zanga-zaga ta barke ana tsaka da shari’ar zaben gwamna a Kano

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gungun masu zanga-zangar da suka mamaye titin da zai sadaka da gidan gwamnatin Kano na cewar suna bukatar Adalci kan batun shari’ar zabe.

 

Masu Zanga-Zangar dai suna rike da alluna dake nuna cewa suna goyon bayan gwamna Kano Abba Kabir Yusuf, inda suke zargin cewa za’a iya yi musu rashin adalci a Shari’ar da ake gudanarwa kan zaɓen gwamnan Kano.

Talla

Mafi akasarin Masu yin Zanga-Zangar yan jam’iyyar NNPP dake rike da gwamnatin jihar kano, wanda hakan ce tasa suma yan jam’iyyar APC dake adawa suka ce suma zasu fito domin yin tasu zanga-zangar don nuna goyon baya ga duk hukuncin da kotu zata yanke.

Da dumi-dumi: NNPP Ta Maka Kwankwaso Kotu Bisa Zargin yiwa jam’iyyar Zagon Kasa

Wannan na zuwa ne yayin da aka baza jami’an tsaro a jihar bisa bayanan sirri na zanga-zanga kan shari’ar zaben gwamna da rundunar yan sanda tace ta samu.

Da dumi-dumi: Tinubu ya Sauyawa Wasu Ministoci Ma’aikatu

Kwamishinan yan sanda na Kano CP Muhammad Usaini Gumel yace sun samu bayanan sirri cewa wasu mambobin jamiyyun siyasa na NNPP da APC sun dakko hayar wasu mutane don yin zanga-zanga a jihar.

Rundunar tace bazata lamunci duk wani yunkuri na kawo tarnaki ga zaman lafiyar jihar Kano ba.

Adai yau ne ake sa ran kotun sauraron korafe-korafe zaben gwamna Kano zata Sanya ranar da zata yanke hukunci kan karar da Jam’iyyar APC ta shigar gabanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...