Daga Hafsat Lawan Sheka
Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Chinedu Ikedieze, wanda aka fi sani da Aki, ya bayyana dalilin da ya sa baya bari a ga iyalansa a shafukan sada zumunta.
Jarumin mai shekaru 45 a duniya ya ce ba ya so matarsa da ‘ya’yansa su shiga shafukan sada zumunta saboda yana son su sami ‘yanci.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da manema labarai .
Ya ce, “Ina da ‘ya’ya amma na yanke shawarar ajiye su a gefe saboda ni ne shahararren, ba su ba.
ECOWAS ta Sanya Ranar da Zata Fara Yakar Jamhoriyyar Nijar
“Ina so kawai su sami ‘yanci saboda duk lokacin da kowa ya san su, zai shafe su, kuma hakan zai sa su rasa ‘yanci, Kuma ba na son hakan.
“Don haka, na boye su har da matata, in ban da a sanarwar bikin aurenmu da aka ganta, kuma daga nan ba a kara ganin ta ba, hakan tasa take iya zuwa kasuwa, ta yi duk abun da take bukatar cikin yanci ba kamar ni ba.”
KADAURA24 ta tuna cewa Ikedieze ya auri masoyoyarsa Nneoma Nwaijah a shekarar 2011.
Ma’auratan sun haifi ‘ya’ya amma dan wasan ya yanke shawarar ɓoye takamaiman adadin ‘ya’yan