Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC , ta ce ta tsare tsohon shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Bukola Saraki.
Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar wa BBC cewa sun gayyaci Sanata Saraki ne domin ya amsa wasu tambayoyi game da zarge-zargen cin hanci.
Sai dai bai yi cikakken bayani kan zarge-zargen da suke yi wa tsohon gwamnan jihar ta Kwara ba.
Amma kafofin watsa labaran kasar sun bayyana cewa ana tuhumar Sanata Saraki ne bisa zarge-zargen sata da halasta kudin haramun.
Sanata Saraki, wanda ya shafe shekaru takwas a matsayin gwamnan jihar Kwara, ya daɗe yana fuskantar zargin cin hanci da kuma halatta kudin haramun.
A baya ya fuskanci shari’a bisa zargin kin bayyana kaddarorinsa amma Kotun Kolin Najeriya ta wanke shi a shekara ta 2018.