Muna fatan Kujerarka zata amfani matasan Kano – Tsofaffin daliban CAS suka fadawa kwamishina kasa

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

Kungiyar tsofaffin daliban makarantar share fagen shiga jami’a ta kano wato CAS aji na shekarar 2003 ta gudanar da liyafar cin Abinci domin taya murna ga daya daga cikin membobinta Hon. Adamu Ali Ibrahim kibiya bisa samun mukamin kwamishina a kunshin gwamnatin jihar Kano.

 

Shugaban kungiyar Aminu kofar mata, yace sun shirya taron liyafar cin abinci ne domin taya murna ga kwamishinan kasa da safayo Hon. Adamu Ali Ibrahim kibiya, bisa mukami da gwamnatin jihar Kano ta bashi, inda ya bayyana sabon kwamishinan a matsayin jajirtaccen matashi wanda yake bada gudunmawa domin cigaban al’umma, ya kuma yi kira a gareshi daya gudanar da ayyukansa bisa gaskiya da rikon Amana.

Talla

Da yake jawabin Kwamishinan kasa da safayo Hon. Adamu Ali Ibrahim kibiya, ya bayyana farin cikinsa bisa wannan karramawa da abokanan karatun sa suka yi masa ya kuma yabawa malaman su bisa irin gagarumar gudanmawar da suka basu a lokacin da suke a matsayin dalibai.

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya Baiwa Dan Wasan Hausa Mukami Mai Gwabi , Tare da Nada Wasu Mutane 13

Yace wannan kujeru da aka bashi ta matasa ce, adon haka yake bukatar yan uwansa matasa dasu taimaka masa ta hanyar bashi shawarwarin da suka dace da kuma addu’o’i domin sauke nauyin da aka dora masa yadda ya dace domin hakanne zai taimaka wajan sake baiwa matasa damammaki a cikin kunshin gwamnati.

Shi ma anasa jawabin daya daga cikin malaman su wadanda suka basu tarbiyya Dakta Auwalu mudi Yakasai yace babban burin malami da kuma iyaye shine su samarda yaya wadanda zasu samu daukaka fiye da tasu inda yaja hankalinsa da rike gaskiya da Amana wajan gudanarda ayyukansa a wannan ma aikata da aka tura shi.

Shi ma daya daga cikin Abokanan karatun sa Alhaji Aminu Attagwa, ya bayyana cewa ma aikatar kasa tana dauke kalubale adan haka yake kira ga kwamishinan da ya kula wajan gudanar da ayyukansa a wannan ma aikata, yace a shirye suke domin bashi gudunmawa data dace wajan sauke Nauyin da aka dora masa ya kuma yi masa fatan alkhairi.

Al’umma da damane suka halarci bikin liyafar cin abinci wadanda suka hadarda Dakta Abdussalam Muhammad kani da Abubakar Ashiru ismail da Hajiya. Maryam Garba wadanda duk tare sukayi karatu a makarantar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...