Zargin Almundahana: Kotu ta dakatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano daga kamawa ko bincikar wasu shugabannin kananan hukumomi

Date:

 

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta dakatar da hukumar karɓar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar daga binciken zargin batan Naira biliyan 100 daga asusun kananan hukumomin jihar.

 

Kotun, karkashin jagorancin mai shari’a S.A. Amobeda, a jiya Talata ta kuma dakatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa da jami’anta daga gayyato, bincike, kamawa, tsoratar da shugabannin kananan hukumomin jihar, har sai an saurari karar da masu nema suka shigar.

Talla

Kotun ta ba da umarnin dakatarwa ne a kan buƙatar da Lauyan masu ƙara Morgan C. Omereonye Esq ya gabatar.

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya Baiwa Dan Wasan Hausa Mukami Mai Gwabi , Tare da Nada Wasu Mutane 13

A jiya Talata ne dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ce ta fara bincike kan zargin karkatar da kudaden da gwamnatin da ta shude ta Abdullahi Ganduje ta yi.

Hukumar ta yi zargin cewa ta bi diddigin yadda aka karkatar da wasu kudaden har zuwa karshe, cikin shekaru hudu.

Majiyar Kadaura24, Daily Nigeria ta rawaito Masu shigar da karar su ne shugabannin kananan hukumomin Dawakin Tofa, Ungogo, Dambatta, Kunchi, Rimin Gado, Karaye, Bichi, Tsanyawa, Gwarzo, Tarauni, Dala, Tudun Wada, Kano Municipal da Shanono 15.

Wadanda ake kara kuma sun hada da hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, da shugabanta Muhuyi Rimin-Gado.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...