A Yau laraba an Fara sauraron Shari’ar Abduljabbar

Date:

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke birnin Kano tana can ta soma shari’ar malamin nan na jihar Sheikh Abduljabbar Kabara.

Jami’an gidan gyaran hali ne suka kai malamin kotu da safiyar Laraba domin a soma shari’arsa a kotun wadda mai shari’a Ibrahim Sarki Yola yake jagoranta.

Ranar Juma’a 16 ga watan Yuli ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.

Wakilin BBC da yanzu haka yake kotun ta Kofar Kudu a birnin Kano ya ce da alama Sheikh Abduljabbar yana cikin koshin lafiya sai dai ya dan rame.

Alkali Sarki Yola ya bayar da umarnin a shiga da Sheikh Albduljabbar cikin akwatin da wanda ake kara ke tsayawa.

Aisha Mahmud ita ce ke jagorantar lauyoyin gwamnatin Kano.

A bangaren Sheikh Abduljabbar, lauyoyinsa sun hada da Sale Mohammad Bakaro, da Yahuza mohd Nura da Bashir Sabi’u, RS Abdullahi, Y I Abubakar, Zaubairu Abubakar, Ya’u Abdullahi Umar, B S Ahmad, da kuma Umar Usman.

Yadda ake zaman kotun na yau Laraba

Alkali Sarki Yola: A ranar farko da aka gabatar da kara, an karnata wa wanda ake karar laifin da ake tuhumarsa da aikatawa, amma ya musanta aikata laifin, ya tambayi shaidu, lauyoyin gwamnati suka ce suna da shaidu bayan an tambaye su ko suna da shaidu.

Alkali Sarki Yola ya tambayi lauyoyin gwamnati shin sun zo da shaidun da suka ce suna da su?

Lauya Aisha: Mun samu dukkan bayanin shari’ar da ake kuma muna neman kotu ta ba mu wata rana domin gabatar mata da shaidu.

392 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...