Daga Rukayya Abdullahi Maida
Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya koka kan dakatar da gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya dakatar da albashin ma’aikata sama da dubu 10 da gwamnatinsa ta dauka aiki.
Ganduje ya koka ne ta cikin wata sanarwa da tsohon kwamishinan yada labarai na jihar kano, Muhammad Garba ya fitar a ranar Laraba, a sakon sa na barka da babbar Sallah ga al’ummar Kano .
Yadda rusau ke ƙara jefa mutane cikin fargaba a Kano
Tsohon gwamnan ya ce dakatar da biyan albashin ma’aikatan da ya dauka aiki ya haifar da damuwa a zukatan ma’aikatan kano, a lokacin da jama’a ke fadi tashin yadda zasu tsira da rayuwarsu .

Kazalika tsohon gwamnan jihar Kanon, ya nuna damuwarsa kan soke karin girma da kuma na matakin albashi da ya yiwa malaman makarantun firamare, da gwamnan kano mai ci ya yi.