Daga Rukayya Abdullahi Maida
Sabon gwamnan jihar kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin gyarawa da inganta cibiyar gyaran hali da tarbiyya deke karamar hukumar Kiru domin magance matsalolin shaye-shaye da matasa ke yi a jihar kano.
” Bai kamata yaran da ake bukatar inganta rayuwar su ace sai sun Rika biyan kudin ba, don haka mun dauke shi zamu cigaba da bada duk abun da ake bukata a wannan cibiya”. Inji Abba Gida-gida
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci cibiyar domin ganin matsalolin da take fuskanta da kuma duba yadda za’a magance su.
Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya Koka da yadda Ganduje ya bar masa bashi Mai tarin yawa
Gwamnan yace gwamnatin sa zata Maida hankali wajen inganta rayuwar matasa domin su ne kashin bayan cigaban al’umma.
Yace shaye-shayen miyagun kwayoyi shi ke haddasa matsaloli na ta’addanci rashin tsaro da saura laifuffuka a cikin al’umma, a don haka yace zai inganta cibiyar ta hanyar samar da ababen more rayuwa da Kuma abinchin da matasan dake gidan zasu rika ci.
Abba Kabir Yusuf wanda ya wannan ziyara ita ce aikin sa na farko bayan rantsar da shi , yace gwamnati ta daukewa Iyayen da yaransu suke karɓar horo, tare da umartar Babbar Sakatariyar ta ma’aikatar mata da ta rubuto masa matsalolin da cibiyar take fuskan domin magance nan da wata guda.
Da take nata jawabin Babbar Sakatariyar ma’aikatar mata ta jihar kano Dr. Sa’adatu Sa’idu Bala ta godewa sabon gwamnan saboda ziyarar da yakai cibiyar wanda tace hakan ya nuna yadda ya damu da halin da matasa ke ciki a jihar kano musamman batun kwacen waya da ake kashe mutane akai.
Babbar Sakatariyar ta bayyana cewa cibiyar tana taka rawa wajen gyara rayuwar matasa ta hanyar basu magani da koya musu sana’o’in dogaro da don inganta rayuwar su. Ta kuma ce cibiyar tana fuskantar matsaloli masu tarin yawa.
Tace ana gudanar da makarantar ne daga Naira 70 da ake biyawa yaran duk wata da kuma Naira dubu dari 5 da tsohuwar gwamnatin kano take ba su.