Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya Koka da yadda Ganduje ya bar masa bashi Mai tarin yawa

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Sabon Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya Koka da yadda tsohon gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje ya bar masa bashin da yakai sama da Naira Biliyan 241 .

” Wanann abun da tsohuwar gwamnati ta yi mana abun takaici ne na bar masa bashin da yakai Sama da Naira Biliyan 241, a Ina za mu samu wadannan kudaden har mu biya”. Inji Abba Kabir

Sabon gwamnan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ya karɓi ragamar mulkin jihar Kano a Gidan gwamnatin Kano.

Abba Kabir Yusuf ya bada tabbacin zai duba yadda gwamnatin tada gabata ta gudanar da mulkin da kuma daukar matakan da suka dace.

” Na zaci tsohon gwamna Ganduje zai tsaya da kansa ya mika mulki kamar tadda aka Saba a nan kano, a Shekarar 1999 Kwankwaso ya mila mulki ga Kwankwaso, Kwankwaso kuma ya mika mulki ga Shekarau a 2003 , haka kuma Shekarau ya mikawa Kwankwaso mulki a Shekarar 2011, shi ma Kwankwaso ya mikawa Ganduje Kwankwaso mulkin a Shekarar 2015 , amma kuma ni Mai yasa ba zai tsaya ya mikamin mulki ba sai dai ya sa wakili ? “. Inji Abba Gida-gida

Engr. Abba Kabir Yusuf ya baiwa al’ummar jihar kano tabbacin gwamnatin sa zata yi duk mai yiyuwa wajen ganin bai basu Kunya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...