Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Zaɓaɓɓen Shugaban kasar Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya karbi bakuncin tsohon firaministan Birtaniya Tony Blair a babban birnin tarayya Abuja.
” Zamu haɗa kai da cibiyar koyar da ingantacciyar gwamnati ta Tony Blair domin samawa al’ummar Nigeria ingantacciyar rayuwa, a kokarin mu na samar da sauƙi ga al’ummar kasa Nigeria”. Inji Tinubu
Tinubu ne ya bayyana hakan a sashihin shafin sa na Facebook a yammacin wannan rana .
” Mun tattauna batutuwan da suka shafi moriyar juna da kuma yadda Najeriya za ta ci gaba da cin gajiyar ayyukan ban mamaki na Cibiyar don kyautata rayuwar al’umma”.
Ana ganin dai Bola Tinubu zai yada kai da cibiyoyi makamantan wannan domin inganta rayuwar al’ummar Nigeria.