Ministocin Buhari sun fara ajiye aikin su gabanin Rusa Majalisar zartarwa ta kasa

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Yayin da ya rage Kwanaki biyar wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kare, ministoci sun fara kokarin mika ragamar ma’aikatunsu ga manyan sakatarorin su gabanin rushe majalisar ministocin, inji rahoton Daily Trust.

 

A ranar litinin 29 ga watan Mayu 2023 wa’adin mulkin shugaba Buhari na shekaru 8, zai kare wanda ya fara daga ranar 29 ga watan Mayun 2015.

An fara gudanar da shirye-shiryen rantsar da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a mako mai zuwa , Inda za a gudanar da taron bikin rantsuwar a dandalin Eagle Square da ke Abuja da misalin karfe 10 na safe ranar.

Da dumi-dumi: Ganduje ya rushe majalisar zartarwarsa

Ana sa ran a yau Laraba Ministan tsaro Bashi magashi zai ajiye aikin sa gabanin Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bada umarnin rushe majalisar zartarwarsa.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa tuni janar Bashir Salihi magashi ya baiwa babban Sakataren ma’aikatar Ibrahim Kana da ya cigaba da tafiyar da ragamar ma’aikatar.

Tsohon Firaministan Burtaniya ya ziyarci Tinubu a Abuja

Wani jami’i a ma’aikatar ya ce ministan ya shaida wa Kana cewa tunda aikin gwamnati ci gaba ne, ya kamata ya tafiyar da duk wasu batutuwan da suka shafi kasafin kudi da kwangiloli bisa tsarin dokar ma’aikatar.

Majiyar Kadaura24 ta rawaito a yau ne za a gudanar da wani liyafar cin abinci domin karrama ministan bisa yadda ya gudanar da aiki a ma’aikatar. A wata sanarwa da ya aike wa daya daga cikin wakilan majiyar ta mu, babban sakatare ya ce Magashi ya cancanci karramawa saboda “salon shugabancin sa”.

“Babban Sakataren ma’aikatar tsaron yace an shirya liyafar cin abincin daren ne don karrama Ministan Tsaro, Janar Bashir Salihi Magashi, bisa la’akari da irin kwazonsa da salon shugabancinsa wajen tsarawa da magance kalubalen da ake fuskanta a fannin tsaro a Najeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...