Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Wata matashir ‘yar shekara 20 mai suna Fatima, a ranar Litinin din nan ta roki wata kotun shari’ar musulunci da ke Kaduna da ta hana mahaifinta, Aliyu Muhammad yi mata auren dole.
Mai shigar da karar ta shigar da karar ne ta hannun lauyanta Malam Y.A Bulama, inda ta shaida wa kotun cewa tana da wanda take so.
lauyan ya shidawa kotu cewa Mahaifin Fatima Yana kokarin Kai ta kauyensu dake jihar Niger don ya aurar da ita ga wani dan uwansu Inda ita kuma tace bata son shi, amma ya dage sai ya aura mata shi .
Kotun sauraren kararrakin zaben shugaba ta bada tabbacin yi wa kowa adalci
Lauyan ya kara da cewa Fatima bata shigar da mahaifin ta Karar don ta tozarta shi ba sai don kotun ta dakatar da shi daga abun da yake shirin yi.
A nasa bangaren, mahaifin Fatimar ya ce iyayensa da suka rasu ne suka zaba wa diyarsa wanda zata aura tun suna raye kuma dole ya mutunta bukatarsu.
Bankwana: Ganduje ya yafewa malaman makaranta kudaden gidaje
“Na aurar da ‘ya’yana mata shida a kauyen kuma suna zaune lafiya da mazajensu, Amma Ina buƙatar kotu ta bani izini don tuntuɓar yan uwana game da wannan batu,” a cewar sa
Alkalin kotun, Malam Isiyaku Abdulrahman, ya ce uba na da ‘yancin zabar wa ‘yarsa mijin aure a karkashin shari’a.
Sai dai ya ce ba a karfafa auren dole yayin da ya shawarci wanda ake kara da ya yi hakuri da abun da ‘yar tasa ta yi.
“Kai ne mahaifinta, don haka ya kamata ka guji yin fushi da ita , inba haka ba baza ta ha daidai a rayuwar ta ba.
“Ka ba ta damar gabatar da wanda take so ta aura kuma idan ka yarda da addininsa da halayensa ka amince ta yi aure shi “, a cewar mai shari’a
Ya kuma shawarci mai korafin da ta zama ‘ya ta gari Mai biyayya da mutunta iyayen ta