Majalisa ta 10: APC ta bayyana sunayen wadanda ta ke so su zama shugabannin majalisar

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Jam’iyyar APC ta fitar da tsarin shiyya-shiyya na mukaman shugabannin da take son su jagoranci a majalisar kasa ta 10 da ke tafe.

 

Babban Kwamitin uwar ayyuka jam’iyyar APC mai mulki ta amince da Sanata Godswill Akpabio daga Kudu maso Kudu da Jubril Barau daga Arewa-maso-Yamma a matsayin shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa a majalisa ta10 .

Haka kuma, shugabannin jam’iyyar APC na kasa sun amince da zabin Hon. Tajudeen Abbas daga Arewa-maso-Yamma da Hon. Benjamin Kalu daga Kudu-maso-Gabas a matsayin kakakin majalisa da mataimakinsa a majalisar wakilai mai zuwa.

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaba ta bada tabbacin yi wa kowa adalci

Jam’iyyar APC ta bayyana matsayin ta ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Felix Morka, bayan wani taron jam’iyyar na NWC a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja a ranar Litinin, don goya baya ga sakamakon ganawar da suka yi da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a baya.

Auren dole: Wata Matashiya ta yi karar Mahaifinta a kotu

Babban Kwamitin ta gana ne domin duba rahotannin tuntubar da tarukan da aka yi a zababben shugaban kasa, da sauran shugabannin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki kan tsarin shiyya-shiyya na rabon mukaman shugabancin majalisar kasa karo ra 10.

“Muna kira ga shugabannin jam’iyyarmu da dukkan ‘yan Najeriya da su ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasarmu a lokacin da kuma bayan lokacin mika mulki a halin yanzu.” A cewar Morka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...