Daga Auwal Alhassan Kademi
Rundunar ‘yan sandan ta kasa ta ce ta kama kwamishinan zaɓen jihar Adamawa da aka dakatar.
Matakin da kwamishinan zaɓen na jihar Adamawa ya ɗauka a lokacin zaɓen 15 ga watan Afrilu ya janyo ruɗani, bayan ya bayyana Binani a matsayin wadda ta yi nasara duk da yake ba a kammala tattara sakamako ba.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce jami’an rundunar masu bibiyar harkokin zaɓe ne suka kama Hudu Ari, ranar Talata a Abuja babban birnin ƙasar.
Ba wani ma’aikaci a Kano da yake bina ko sisin kobo – Ganduje ya bugi Kirji
sanarwar ta ce kwamishinan na INEC yana hannunta don amsa tambayayoyi kan tuhume-tuhumen da ake masa game da ayyana Sanata Aishatu Binani a matsayin wadda ta yi nasara a zaɓen cike giɓi da aka gudanar ranar 15 ga watan Afrilu.
Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya ce rundunar za ta kama duk mutanen da ke da hannu a lamarin domin gudanar da bincike kamar yadda doka ta tanada.
Hajjin bana: Jirgin Max Air NAHCON ta baiwa aikin jigilar maniyyatan Kano – Abba Danbatta
Ya kuma sake jaddada ƙudurin ‘yan sandan wajen tabbatar da adalci a cikin lamarin tare da gurfanar da duk mutanen da ke da hannu a lamarin gaban kotu.
Lamarin ya sanya hukumar zaɓe ta INEC ta dakatar da Ari, yayin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da umurnin gudanar da bincike a kan sa, da kuma jami’an tsaron da suka ba shi kariya a lokacin da abin ya faru.
A wata ganawa da manema labarai Hudu Ari ya musanta zargin da ake yi cewa ya karɓi cin hancin naira biliyan biyu, kafin ayyana Sanata Aishatu Binani a matsayin wadda ta yi nasara.