Hajjin bana: Jirgin Max Air NAHCON ta baiwa aikin jigilar maniyyatan Kano – Abba Danbatta

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON, ta baiwa kamfanin Max Air aikin jigilar maniyyatan jihar Kano su 5,917 zuwa kasar Saudiyya yayin aikin hajjin bana.

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa matakin da NAHCON ta dauka na baiwa kamfanin Azman Air jigilar maniyyatan jihar a shekarar da ta gabata ya fuskanci gagarumar suka daga hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano da gwamnatin jihar.

 

Kamfanin Max Air dai ya dade yana jigilar alhazan jihar zuwa aikin Hajji har zuwa shekarar da ta gabata a lokacin da sabon shugaban hukumar NAHCON ya baiwa kamfanin Azman Air aikin jigilar.

A wata ganawa da manema labarai a ranar Talata, sakataren zartarwa hukumar jin dadin alhazai ta jihar kano, Muhammad Abba Dambatta, ya bayyana cewa hukumar alhazan ta kasa ta baiwa kamfanin Max Air aikin hajjin bana.

Masarautun kano 5 nan gani nan bari – Gwamna Ganduje

Ya kara da cewa jirgin yana da inganci kuma yana da jiragen sama guda uku masu daukar da maniyyata sama da 1,000 kowanne, wanda hakan zai samar da sauƙi ga maniyata aikin hajjin bana.

 

Hakazalika, Dambatta ya kuma sanar da cewa hukumar ta rufe sabon rajistar aikin Hajjin sakamakon umarnin da NAHCON ta bayar.

A cewarsa, hukumar ta Sami kujeru kusan 6,000 da hukumar NAHCON ta ware mata, inda ya kara da cewa maniyyata 4,900 sun kammala biya kudin aikin Hajjin baki daya, yayin da sauran wadanda suka ajiye Naira miliyan 2.5 za su cika sauran kuɗin nan da kwanaki masu zuwa.

Sakataren zartarwa ya kuma bayyana cewa hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da aikin Hajjin bana, yana mai cewa “mun kammala dukkan shirye-shirye tun daga wurin kwana, ciyarwa, jigilar kaya daga Jeddah zuwa Makkah da Makkah zuwa Madina.

Mun shirya don hawan jirgi. Mun yi tsari mai kyau wanda zai tabbatar da kudin da mahajjatan mu ka biya, Mahajjatan mu za su yi rayuwa mai kyau a Saudiyya,” Dambatta ya tabbatar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...