Ba wani ma’aikaci a Kano da yake bina ko sisin kobo – Ganduje ya bugi Kirji

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar kano ya bugi kirce tare da fadin cewa ba Wani ma’aikacin gwamnatin jihar kano da yake bin gwamnatin sa ko sisin kobo.

 

” Tun da na zama gwamnan kano a Shekarar 2015 ba wani wata da ya zo ya wuce ban biya ma’aikata kudin albashinsu ba, duk kuwa da matsalolin tattalin arzikin da aka rika fuskanta a lokuta daban-daban”. Ganduje

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake bankwana da ma’aikatan jihar kano, a ranar bikin ranar ma’aikata ta bana.

Masarautun kano 5 nan gani nan bari – Gwamna Ganduje

” Kun Sani cewa anyi karin albashi na Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi , mu a Kano har wani abu muka kara akan dubu 30 din kuma tun wancan lokacin har zuwa yanzu bamu taba bashin biyan albashi ba, saboda haka ma’aikatan gwamnatin jihar kano na yi shekara 8 babu mai cewa yana bina ko sisin kobo a wajen harkar albashi”. A cewar Ganduje

Ranar Ma’aikata: Zamu inganta rayuwar ma’aikatan gwamnati, ta Biyan Albashi da Fansho cikin gaggawa– Abba Gida-gida

Yace gane da biyan kudaden kammala aiki sun gaji bashi mai yawa hakan tasa bashin kudin ya kara karuwa saboda ba’a iya daukar ma’aikata, Amma yace gwamnatin sa ta fito da wani tsarin wanda zai yi maganin wannan matsala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...