Cutar Lassa ta kashe mutune sama da 150 a Najeriya – NCDC

Date:

Daga Safiyanu Dantala Jobawa

 

Cibiyar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya NCDC ta ce cutar zazzaɓin lassa ta halaka mutum 154 a cikin jihohin ƙasar 26 tun farkon shekarar da muke ciki.

 

A cikin rahoton yanayin cutar da cibiyar ta fitar ranar Litinin, NCDC ta ce a cikin watanni huɗun farko na shekarar 2023, an samu masu ɗauke da cutar 897.

Cibiyar ta ce jihohin da aka samu cutar sun haɗar da Ondo da Edo da Bauchi da Taraba da Benue da Plateau da Ebonyi da Nassarawa da Kogi da Taraba da Gombe da Enugu da Kano da Jigawa da sauransu.

Ba wani ma’aikaci a Kano da yake bina ko sisin kobo – Ganduje ya bugi Kirji

Rahoton ya ce, “tun daga satin farko zuwa 16 a wannan shekarar an samu mutuwar mutum 154”.

NCDC ta ce an samu kashi 72 cikin 100 da cutar a jihohi uku da suka haɗar da Ondo da Edo da kuma Bauchi, inda ka samu kashi 28 daga jihohi 23.

Rahoton ya ce adadin masu ɗauke da cutar ya ƙaru idan aka kwatanta da daidai wannan lokaci a shekarar 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...