Daga Rukayya Abdullahi Maida
Yayin da al’ummar Musulmi ke bikin Sallar karama a yau, Kungiyar ‘Yan Jaridu ta kasa reshen jihar Kano (NUJ) ta bukaci shugabannin da aka zaba da
su sanya kasar a gaba a kokarinsu a na magance kalubalen da suke fuskanta .
Hakan na kunshe ne a cikin sakon barka da Sallah da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Kwamared Abbas Ibrahim da Sakatarenta Malam Abba Murtala, kuma aka rabawa manema labarai a Kano.
“muna kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da goyon baya ga tsarin dimokaradiyya, NUJ na yin kira ga zababbun shugabanni da su sanya kasar nan a gaba ta hanyar fito da tsare-tsare masu inganci da zasu magance kalubalen tattalin arziki, zamantakewa da siyasa a kasa,” in ji kungiyar.
Ƙungiyar tana taya al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar Sallah karama, sannan kungiyar ta yi kira gare su da su yi koyi da darussan da suka koya a watan Ramadan da suka hada da soyayya, sadaukarwa, zaman lafiya da ‘yan uwantaka a yayin da kasar nan ta shigo sabon tsarin dimokradiyya.
Ƙungiyar ta yaba da rawar da ‘yan jaridu da hukumomin tsaro da kungiyoyin farar hula da INEC da masu zabe da sauran masu ruwa da tsaki suka taka a zaben da aka kammala a jihar da ma kasa baki daya.
Daga nan sai kungiyar ta jaddada bukatar ‘yan kasar da su kasance masu taka-tsan-tsan da kuma kai rahoton duk wani motsi da basu aminta da shi ba ga jami’an tsaro.
An yi addu’ar Allah ya sa a yi bukukuwan karamar Sallah lafiya da kuma samun damina mai albarka.