Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya ce cutar kansar baki da aka fi sani da kansar baka, na kashe mutane 764 a Najeriya duk shekara.
Ministan ya bayyana hakan ne jiya a Abuja yayin wani shirin horas da mutane yadda zasu kare kansu daga cutar kansar baka wanda gidauniyar Cleft and Facial Deformity Foundation (CFDF) ta shirya.
Bankwana: Gwamna Ganduje ya nemi afuwar al’ummar jihar kano
Shugabar sashin kula da hakora na ma’aikatar lafiya, Dr Gloria Uzoigwe, ce ta wakilci minjstan, ta ce Najeriya kuma na samun sabbin masu kamuwa da cutar daji guda 1,146 a duk shekara.
Ya ce ciwon daji na baki ya kasance daya daga cikin abubuwan da ke haifar da mace-mace mutane masu alaka da cutar daji a Najeriya saboda jinkirin rahoton da ake samu a asibitoci, da gazawar jami’an kiwon lafiya wajen gano cutar da wuri da kuma rashin isar da sako yadda ya kamata da dai sauransu.
Ministan ya ce gwamnati za ta kaddamar da wani sabon shirin kula da lafiyar baki a watan Nuwamba.