Tsawa ta kashe a ƙalla mutum 16 tare da jikkata wasu da dama a garin Jaipur da ke arewacin Indiya a ranar Lahadi.
Mutanen suna ɗaukar hoton “selfie” ne a cikin ruwan da ake sheƙawa a saman wata hasumiya da ke wani gini mai tarihi na yawon buɗe ido.
Mutum 27 ne ke kan ginin da kuma bangon a lokacin da abin ya faru, kuma rahotanni sun ce wasu daga cikin su sun yi tsalle sun faɗa ƙasa.
A ƙalla mutum 2,000 tsawa ke kashewa duk shekara a Indiya.
Wani babban jami’in ɗan sanda ya shaida wa kafafen yaɗa labarai cewa mafi yawan mutanen da suka rasun matasa ne.

A ranar Lahadi kaɗai an samu rahotannin mutuwar mutum tara a faɗin jihar Rajasthan inda Jaipur yake, a cewar kafofin yada labaran yankin.
Rahotanni sun ce ana kuma samun rahotannin mutuwa a sauran jihohi sakamakon faɗuwar tsawa.
An ruwaito cewa a ƙalla mutum 41 – mafi yawa mata da yara ne tsawa ta kashe a gundmomin jihar Uttar Pradesh. Mafi yawan waɗanda suka rasun mutum 14 a birnin Prayagraj suke.
Manyan ministocin Uttar Pradesh da Rajasthan sun sanar da biyan dala 6,700 a matsayin diyya ga iyalan waɗanda suka rasun.
Ofishin Firaminista Narendra Modi ma ya sanar da biyan dala 2,681 ga iyalan mamatan a dukkan jihohin uku.