Gayyatar da mu kaiwa Abduljabbar Bata da alaka da Mukabala-DSP Kiyawa

Date:

Rundunar ƴan sanda ta Kasa reshen jihar Kano ta gayyaci Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayyana a gabanta a ranar Litinin 12 ga watan Yuli don amsa wasu tambayoyi kan ƙararsa da wani malamin ya kai.

Hakan na zuwa ne kwana biyu bayan kammala muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da wasu Malaman Kano.

Sai dai kakakin ƴan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce gayyatar da suka yi wa Malam Abduljabbar Nasir Kabara ba ta da alaƙa da muƙabalar da aka yi da shi ko kalaman da malaman jihar ke zargin sa da yi.

“Wannan gayyata ba ta da alaƙa da wannan zama da aka yi, dama tun kafin a yi wannan zama akwai waɗanda suka shigar da ƙorafe-ƙorafe a kansa, kuma an fara bincikawa, in ji Kiyawa.

DSP Kiyawa ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike.

“Dama an sa ranar dawowa don ci gaba da binciken, to kuma yau ce ranar kamar yadda aka sa a baya,” ya ƙara da cewa.

315 COMMENTS

  1. Энтони Джошуа и Александр Усик прошли процедуру взвешивания перед боем, который состоится 25 сентября. Прямой эфир на телеканале Рен-ТВ. Вес: Александр Усик — 100,2 кг; Энтони Джошуа — 108,9 кг ПРЯМАЯ ССЫЛКА НА ВИДЕО В этом Александр Усик Энтони Джошуа DAZN Усик Джошуа – мощное промо боя, видео – Новости бокса

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...