Bayan karbar Sammaci, Rarara ya gurfana a gaban kotu

Date:

 

Wata babbar kotun shari’ar musulinci dake zaman ta a unguwar Rijiyar zaki Kano, ta baiwa lauyoyin Dauda Adamu Kahutu Rarara damar yin nazari kan da’awar mai ƙara ta naira Miliyan 10 da dubu ashirin da uku da ɗari tara ,na kuɗaɗen wayar da yake karɓa bashi yana rabawa ga al’umma.

 

Wanda yake ƙara Muhammad Ma’aji , ya ce sun ɗauki lokaci da mawaki Dauda Rarara yana karɓar wayoyin salula a wajensa Inda yake rabawa ga yaransa da kuma mutanen gari”.

 

“A farkon haɗuwar mu idan ya karɓi wayoyin nan take yake biya na kuɗin, amma bayan mun saba sai dai ya kirawo ni a waya yace , wani zai zo ya karɓi waya ko kuma ya bani sunayen mutanen da za a baiwa”. A cewar mai kara

Yan takarar majalisar jiha na NNPP su 9 a Kano sun yi karar APC, INEC a Kotun sauraren kararrakin zabe

Mai ƙarar ya ƙara da cewa a baya, ba shi da shamaki da Rararan, domin ko wanne lokaci ya kira shi yana ɗaga wayarsa, amma daga bisa sai ya daina daga wayarsa kimanin shekara ɗaya da watanni uku kenan.

FCE Bichi na daf da durkushewa, saboda matsalolin da suka yi yawa a makarantar – Dr. Hussaini Peni

 

” bayan ɗauke ƙafa da nayi na daina zuwa inda yake , sai ya zo har ofins ɗina ya ce gobe zai bani kuɗin domin sun taru da yawa sai dai har yanzu bai bayar ba.

 

” kuma ni ne nake sanya wa iyalansa da yaransa ƴan social media Katin TV , Data, bisa alƙawari da muka yi da shi .

 

Lauyan mawaki Dauda Rarara Barr. G.A. Badawi ya roƙi kotun ta basu damar yin nazari a kan da’awar mai ƙara da kuma tuntuɓar mai ƙarar.

 

Tuni dai Kotun ta amince da roƙon lauyan wanda aka yi ƙara .

 

Mai shari’a Mallam Halhalatul Kuza’i Zakariyya ya dage shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Afrilun 2023.

 

Oddity24

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...