An kori ‘yan sandan da ke yi wa mawaki Rarara rakiya

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kori wasu jami’anta guda uku daga aiki bayan ta same su da laifukan rashin ɗa’a da kuma yin amfani da bindiga ba yadda ya kamata ba.

 

A Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta ce an samu ‘yan sandan ne da aikata abubuwan da ka iya zubar da mutuncin rundunar, inda suka yi amfani da makami ta hanyar da ba ta dace ba, da tozarta muƙamansu, da nuna tsagwaron rashin ɗa’a, da kuma ɓarnata harsasan gaske.

FCE Bichi na daf da durkushewa, saboda matsalolin da suka yi yawa a makarantar – Dr. Hussaini Peni

 

Ta ce ‘yan sandan suna aiki ne da wani mawaƙi a Kano lokacin da aka tura su don ayyukan rakiya da bayar da kariya.

 

Ta ce matakin na zuwa ne bayan ƙorafe-ƙorafe da kuma binciken da aka yi kan wata shaidar bidiyo da aka yayata sosai ranar 7 ga watan Afrilun 2023 a shafukan sada zumunta.

 

Bayan karbar Sammaci, Rarara ya gurfana a gaban kotu

Ta ce matakin na zuwa ne bayan ƙorafe-ƙorafe da kuma binciken da aka yi kan wata shaidar bidiyo da aka yayata sosai ranar 7 ga watan Afrilun 2023 a shafukan sada zumunta.

 

A cewarta, an zargi ‘yan sandan uku – na sashen ba da kariya ta musamman (SPU) da suka haɗar da Sufeto Ɗahiru Shu’aibu da Saje Abdullahi Badamasi da Saje Isah Ɗanladi – da zafin hannu, da halayyar rashin ƙwarewa, da amfani da makami ta hanyar da ba ta dace ba.

 

Daga nan ne kuma rundunar ta yi wa ‘yan sandan da abin ya shafa shari’a, inda aka same su da laifi kuma aka kore su.

 

Sanarwar ta ce a ranar Juma’a 7 ga watan Afrilun 2023 ne ‘yan sandan suka yi harbe-harbe cikin iska a ƙauyen Kahutu da ke jihar Katsina, duk da manufar aikin ‘yan sanda da ke hana su yin hakan.

 

Ta ce abin da kuma suka yi, ya saɓa wa tsarin ƙa’ida na gudanar da aikinsu da kuma jerin umarnin rundunar masu alaƙa.

 

Sanarwar CSP Olumuyiwa ‘yan sandan da aka kora daga aiki sun kuma yi biris da hatsarin da za a iya samu lokacin da suka yi harbi sama cikin mutane cincirindo da suka haɗar da ƙananan yara.

 

Ta ce harbe-harben da ‘yan sandan suka yi, ba kawai laifi ba ne, abu ne kuma da ke nuna rashin ƙwarewar aiki, da kunyata rundunar ‘yan sanda da Najeriya gaba ɗaya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...