Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
Shahararren mawakin nan Kuma Shugaban kungiyar 13 -13 Dauda kahutu Rarara yace wasu matasa ne suka yi yunkurin tada hatsaniya a Inda yake rabon kayan abinchin a karinsu, shi ne dalilin da yasa jami’an tsaron fake gadin sa suka harba bindiga sama don tsarwatsa su.
Mun kama yan sandan dake gadin mawaki Rarara – Rundunar yan sanda
” Mun je kahutu Muna raba kayan azumi kamar yadda muka saba , sai ga wasu matasa nan suka zo wajen zasu tayar mana da hatsaniya Kuma kaga azumi ne yan sanda baza su sa tiyagas ba, to shi ne sukai harbi sama don tarwatsa su”. Inji Rarara
Rasuwar Matar Aminu Dantata babban rashi ne ga jihar kano Inji Gwamna Ganduje
Kadaura24 ta rawaito Dauda kahutu Rarara ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da manema labarai.
Yace ya yi kokarin nunawa yan sandan cewa ba Wani abu saboda mahaifarsa ce , Amma dai yayi zargin cewa matasan za suka je wajen ba yan garin ba ne daukar nauyin su Akai domin su je su tayar musu da hatsaniya.
” Ina baiwa matasa shawara su daina bari yan siyasa suna amfani da su wajen tada tarzoma, saboda idan kuka yi tunani wanda ya sa ku wannan aikin ba hado ku da ‘ya’yan sa ba , daga haka zaku fahimci ba aikin kwarai ya Saka ku ba”. A cewar Rarara