Daga Aisha Aliyu Umar
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya mika ta’aziyyarsa ha hamshakin dan kasuwanan kuma guda cikin dattawan kano Alhaji Aminu Alhassan Dantata da daukacin iyalan Dantata bisa rasuwar uwargidansa Hajiya Rabi Aminu Alhassan Dantata.
Ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa ta gari waccce ta bada rayuwar ta wajen tarbiyantar da makusantanta bisa gaskiya da rikon amana.
“Hajiya Rabi Aminu Alhassan Dantata uwa ce mai kauna ga kowa, wadda adalcinta ya bata damar jagoranci ga wadanda ke kewaye da ita,” Ganduje ya yaba mata.
Mun kama yan sandan dake gadin mawaki Rarara – Rundunar yan sanda
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Malam Abba Anwar ya aikowa kadaura24.
Gwamna Ganduje ya kara da cewa, “A madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga babban jigonmu, uba mai hangen nesa, Alhaji Aminu Alhassan Dantata bisa rasuwar marigayin. Hajiya Rabi Aminu Alhassan Dantata.”
Gwamna Ganduje ya bayyana rasuwar a matsayin “… babban rashi ne ba ga iyalanta kadai ba, har ma ga jihar da kuma sauran al’ummar salihai. Kamar yadda muke kaunar kasancewarta a tsakaninmu, Allah Ta’ala Ya fi kaunarta. Don haka. lokacinta a duniya ya wuce.”
“Allah Ya jikanta da Rahma, Ya kuma sa ta hutu ya yi mata sakamako da gidan Jannatul Fiddaus, Ya duba abin da ta bari”. A cewar Ganduje