Daga Kamal Umar Ali
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce an gano wasu masu rakiyar fitaccen mawakin nan na Kano, Dauda Kahutu Rarara a cikin wani faifan bidiyo suna harba bindiga a iska, a cikin al’umma, Kuma tuni an kama su.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda ta kasa CSP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Alhassan Ado Doguwa ya yi Nasara, Kotu ta bada umarnin karasa zaben Tudun Wada da Doguwa
CSP Adejobi ya bayyana cewa, “Mun fara daukar matakan ladabtarwa a kansu. Za su gana da IGP a Abuja ranar Talata. Tabbas, za a hukunta su .”
Ba a son raina zakara ya haɗa ni faɗa da makwabcina ba – Mai zakaran da kotu ta ce a yanka
Idan za’a iya tunawa wani video ya karade kafafen sada zumunta na zamani Inda aka ga yan sandan suna harbi sama ,Amma a cikin bidiyon ba wanda zai ce ga dalilin da ya sanya yin harbin.
Hakan dai ya jo cheche-ku ce tsakanin al’umma musamma a dandalin sada zumunta, Inda wasu ke nuna goyon baya wasu Kuma suke ganin hakan bai kamata ba, kamar a kwai ranar da al’umma a cikin lamarin.