Daga Al-Ameen Sa’eed Bichi
Babantunde Raji Fashola Ministan ayyuka da Gidaje, ya bayyana cewa aikin gina titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano zai wuce wa’adin mulkin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da zata kare nan da 29 ga watan mayu.
Sai dai kuma Fashola, wanda ya bayyana haka a yayin ziyarar duba aikin gadar Loko-eweto a jihar Nasarawa a ranar Laraba, ya ce za a kammala titin Legas zuwa Ibadan a ranar 30 ga Afrilu.
A cewar Fashola, titin Abuja-Kaduna-Kano ya kasance mafi girman dukkan ayyukan titin ta fuskar girma da kuma kudi da gwamnatin Buhari ta bayar.
“Abuja-Kano ita ce mafi girma a cikin ayyuka uku ta fuskar girma, ta fuskar kasafin kudi; shi ne kilomita 375.
“Ya ƙunshi gadoji 41 masu girma daban-daban. Shi ne na ƙarshe don farawa, don haka ba zai iya gamuwa a lokaci guda ba. Wannan ita ce magana ta gaskiya.
“Amma mun samu ci gaba daga Zariya zuwa Kano, wato kilomita 137, kuma ‘yan kwangilar sun shaida mana cewa ya zuwa ranar 15 ga watan Mayu za a kammala aikin.
“Sai kuma muna da Kaduna zuwa Zariya, mai nisan kilomita 70 da wani abu. Shi ma wannan bangaren, sun ce za a kammala shi a ranar 30 ga wannan wata, kuma za a bude su baki daya domin al’umma su ci gaba da amfani da su,” inji shi.