El-Rufai ya mayar da malaman da ya kora bakin aiki

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

Gwamnatin Kaduna ta amince a mayar da malaman makarantar firamare fiye da duɓu ɗaya da ta sallama a Yunin 2022 bayan yi musu wata jarrabawar tabbatar da ƙwarewarsu.

Kakakin ma’aikatar ilimi ta jihar Hajiya Hauwa Muhammad ce ta bayyana hakan cikin sanarwar da aka fitar yau Laraba.

Hajiya Hauwa ta ce malamai 1,266 ne aka yi wa jarrabawar gwajin cancantar yayin da 22 a cikinsu aka tsame su daga jadawalin albashin gwamnati.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa a Yunin 2022 ne ma’aikatar ilimin ta kori malaman Firamare 2,357 saboda gaza tsallake jarrabawar.

Ita ma jaridar Punch ta ruwaito ma’aikatar ta yi bayanin cewa an sallami malamai 2,192 saboda ƙin rubuta jarabawar yayin da malamai 165 kuma aka kore su saboda rashin tabuka abin a zo a gani.

Wasu daga cikin malaman da matakin ya shafa sun yi ƙorafin cewa sun rubuta jarrabawar kuma sun ci kuma duk da haka aka kore su yayin da wasu kuma suka yi iƙirarin cewa ba su da lafiya a lokacin da aka yi jarabawar kuma sun gabatar da takardar shaida.

Su kuwa wasu malaman cewa suka yi an yi garkuwa da su ne a lokacin, yayin da wasu suka ce a lokacin an dakatar da su ne saboda aikin tantance takardunsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...