Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin yin duk mai yiyuwa wajen ganin jihar ta cigaba da rike kambunta na jihar da tafi kowacce jihar yawan mutane, yayin aiki ƙidayar da za’a gudanar a bana.
Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan lokacin da yake kaddamar da yan kwamitin yada labarai wanda gwamnatin kano kafa domin wayar da akan al’umma muhimmancin kidayar.
Mun yi takaicin yadda muka rasa kujerar gwamnan kano – APC
Gwamna Ganduje wanda Sakataren gwamnati jihar Alhaji Usman Alhaji ya wakilta yace gwamnatin Kano ta ɗauki sha’anin kidayar da matukar muhimmanci, domin idan kana tafi kowacce jihar yawan mutane to zata Fi su amfana daga rabon tattalin arzikin kasa .
Sarkin Kano ya Jagoranci Sallar Jana’izar Matar Gwamnan Kano na farko
Yace an kafa kwamitoci da dama wadanda zasu taimaka wajen ganin an sami nasara kidayar ta bana, Kuma kwamitoci sun haɗa rukunonin al’umma daban-daban domin baiwa kowa damar bada tasa gudunmawar.
Yace za’a yi kidayar ne a makon farko na watan mayu wanda Kuma hakan ya nuna cewa lokacin gwamnatin Ganduje ce ke kan mulki , Amma duk da haka ta turawa Sabon zababben Gwamnan Kano da ya turo da wakilai wadanda za’a gudanar da aikin tare da su , saboda idan su ka zo mulki zasu samin cikakken bayanin abun da akai .