Sarkin Kano ya daga likkafar wasu hakimansa tare da nada sabbi

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya daga Darajar wasu Hakimansa da kuma nada wasu sababbi.

 

Daga cikin Hakiman da aka daga Darajarsu sun hasar da Sarkin Dawakin Tsakar Gida Alhaji Ahmad Ado Bayero zuwa Dan Iyan Kano da Turakin Kano Alhaji Lamido Sunusi Bayero zuwa Sarkin Dawakin Tsakar Gida.

 

Tafidan Kano Alhaji Mahmoud Ado bayero ya zama Turakin Kano yayinda Dan Galadiman Kano Alhaji Haruna Rasheed Sunusi aka daga Darajarsa zuwa Tafidan Kano, sai Alhaji Kabiru Tijjani Hashim Dan Isan Kano ya zama Dan Galadiman Kano.

 

Ina godiya ga yan jaridu bisa hadin kan da suka ba ni – inji mai magana da yawun Ganduje Abba Anwar

Sauran sune Dan Lawan din Kano Alhaji Bashir Ado Bayero ya koma Dan Isan Kano, Alhaji Yahaya Inuwa Abbas Dan Majen Kano ya zama Lawan din Kano.

Abba Gida-gida ya shawarci  masu gine-gine a wararen Gwamnatin kano da su dakata

 

Kazalika Mai Martaba Sakin ya nada Alhaji Ahmad Kabiru Bayero a Matsayin Barde Kerarriya da kuma Alhaji Abdulkadir Mahmoud a Matsayin Magajin Rafin Kano.

 

A wata sanarwa da Sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24, yace jin kadan da nadasu, Mai Martaba Sakin yace an basu wadannan Sarautu ne saboda cancantaru da kuma hidimtawa al’umma.

 

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukace su zamo jakadu nagari a duk inda suka sami kansu tareda ciyar da masarautar ta Kano gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Bam ya fashe a Kano ya hallaka wasu ya kuma jikkata wasu

Aƙalla mutum biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin...

Kotu a Kano ta sami wani Tela da laifin takurawa makwabtansa da karar keken dinki

Wata kotu a Kano ta samu wani tela da...

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...