Dakatar da gine-gine: Ka jira a rantsar da kai kafin ka fara bada umarni – Ganduje ya fadawa Abba Gida-gida

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnatin Kano ta yi kira ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi haƙuri, ya daina baiwa al’ummar jihar kano umarnin da sunan shawara ga jama’a, Saboda irin wannan shawara za ta iya haddasa ruɗani na babu gaira babu dalili a cikin jihar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar kano, Muhammad Garba ya fitar don maida martani ga zaɓaɓɓen gwamnan a kan batun dakatar da gine-gine a wurare mallakin gwamnatin kano.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa zaɓaɓɓen gwamnan kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya baiwa Masu gine-gine a wuraren gwamnatin shawarar su dakatar da hakan ko kuma duk abun da ya biyo baya su yi kuka da kansu.
Gwamnatin Kano ta ce abin da zaɓaɓɓen gwamnan ya yi na bayar da umarni kan abun da hurumi ne na gwamnatin ba dai-dai bane, saboda har yanzu Dr  Abdullahi Umar Ganduje sh ne gwamnan jihar gar ranar 29 ga watan mayu wanann shekara ta 2023.
Ta ƙara da cewa kamar yadda yake ƙunshe a cikin tsarin mulkin Najeriya, Dr. Abdullahi Umar Ganduje zai ci gaba da zama gwamna mai cikakken iko har zuwa ranar 29 ga watan Mayu, kuma yana da damar gudanar da ayyukansa hatta a ranar jajiberen saukarsa daga mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...