Daga Maryam Ibrahim Zawaciki
An tsaurara tsaro a jahoji 28 cikin jahohi 36 na Najeriya inda za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jahohi a gobe Asabar.
Babban sifeton ‘yan sandan Najeriyar, Usman Baba, ya ayyana dokar hana zirga-zirgar ababen hawa a jahojin daga karshe 12 na tsakar daren Juma’a har zuwa karfe shida na yammacin ranar Asabar bayan kamala zaɓukan.
Rahotanni sun ce an samu hatsaniya a tsakanin magoya bayan jam’iyyu a Jahar Legas, inda gwamnan Jahar mai ci na jam’iyyar APC, Babajide Sanwo-Olu, yake fuskantar zazzafar adawa daga ɗan takarar gwamnan Jahar na jam’iyyar Labour, Gbadebo Rhodes-Vivour.
Jam’iyyar ta Labour ce dai ta samu kuri’u mafi yawa a zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana watan jiya.