Khadija Abdullahi Aliyu
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP ya bukaci al’umma suyi amfani da damar da suke da ita wajen zabar shugabanni nagari wadanda zasu jagoranci al’umma.
Sarkin yayi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi na musamman ga manema labarai a fadarsa.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’uma dasu zauna lafiya a lokutan babban zabe na kasa da za’a gudanar a ranar asabar mai zuwa.
Sarkin yace sai daΒ zaman lafiya ne ake iya aiwatar da komai, a don haka ne ya bukaci matasa su kaucewa furta munanan kalamai da amfani muggan makamai tare da shan kayan maye da dukkan wani abu daka iya jirkitar da hankalinsu domin kaucewa abubuwan da basu kamata ba.
A sanarwar da Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24 yace, Alhaji Aminu Ado Bayero ya sake jaddada bukatar Hakimai da Dagatai da masu anguwanni su cigaba da wayar dakan al’umarsu muhimmacin Zaman lafiya.
Yayi kira ga jamiβan tsaro dasu cigaba dasa ido akan dukkan wanda ya aikata wani lafi tare da hukuntashi,
Alhaji Aminu Ado Bayero yayi addu’ar samun zabin shugabanni nagari a dukkan matakan zabubbukan da za’a gudanar a fadin kasar nan.