Gabanin zaben gwamnoni da na yan majalisu, yan Sanda sun tsaurara tsaro a Najeriya

Date:

Daga Maryam Ibrahim Zawaciki

An tsaurara tsaro a jahoji 28 cikin jahohi 36 na Najeriya inda za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jahohi a gobe Asabar.

Babban sifeton ‘yan sandan Najeriyar, Usman Baba, ya ayyana dokar hana zirga-zirgar ababen hawa a jahojin daga karshe 12 na tsakar daren Juma’a har zuwa karfe shida na yammacin ranar Asabar bayan kamala zaɓukan.

Ku yi amfani da damar ku wajen zabar shugabanni nagari don inganta rayuwar ku – Sarkin Kano ya fadawa al’ummar sa

Rahotanni sun ce an samu hatsaniya a tsakanin magoya bayan jam’iyyu a Jahar Legas, inda gwamnan Jahar mai ci na jam’iyyar APC, Babajide Sanwo-Olu, yake fuskantar zazzafar adawa daga ɗan takarar gwamnan Jahar na jam’iyyar Labour, Gbadebo Rhodes-Vivour.

Jam’iyyar ta Labour ce dai ta samu kuri’u mafi yawa a zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana watan jiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...