An kaddamar da Kungiyar Masu gabatar da shirye-shiryen al’amuran Yau da kullum a Kano

Date:

Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa

An bukaci Shuwaganni Kungiyar masu gabatar da shirin shirye-shiryen al’amuran Yau da kullum (Magazine programme) a Jihar Kano, dasu zamo masu kwatanta adalci da yin aiki tukuru.

Bayanin Hakan ya Fito ne Cikin Wata sanarwa da Jami’in Hulda da jama’a na Kungiyar Yusuf Ali Abdullah ya aikowa Kadaura24, Inda yace an gudanar da Taron kaddamar da Shuwaganni Kungiyar,Wanda ya gudana a gidan Radio Pramid.

Yusuf Ali Abdullah ya kara da cewa lokaci yayi da Masu gabatar da shirye shiryen zasu zamo tsintsiya madaurin ki daya, da kuma temakon Al,umma a cikin rayuwa.

Inda ya bukaci Shuwaganni wannan jiha dasu bawa Kungiyar goyan bayan daya kamata domin kawo karshen matsaloli da Suke damun Al,umma.

Tun da fari a nasa jawabin Mai rikon mukami. Shugabancin Kungiyar Gidajen Radio 13 masu gabatar da shirin Magazine programme, Sani Abdurrazak Darma,ya godewa Allah bisa bashi dama ya zama Shugaban Kungiyar, inda ya roki Duk Gidajen Radio a Kano su basu goyan Baya ,,domin inganta Shirye shiryen .

Sani Abdurrazak Darma yayi Alkawari zai kiyaye Duk wasu abubuwa da zasu kawo matsala a cikin Kungiyar tare da kwatanta adalci a tsakanin ‘yan Kungiyar.

Kakakin Kungiyar ya rabawa manaima labarai Wato Yusif Ali Abdallah ya bayyana cewa an zabi Shugabanni da zasu Jagoranci Kungiyar Mai Suna Magazine Radio Kano forum.

🎧MAGAZINE RADIO KANO FORUM🎧

JERIN SUNAYEN SHUWAGABANNI

1- Sani Abdurrazak Darma Express Radio… Chairman

2- Rukayya Abdullahi Maida Guarantee Radio..Vice Chairman.

3- Abubakar Abdulkadir Uran Radio Kano… Secretary

4- Sharif Ahmad Sidi Vision Radio…. Treasure

5- Musa Mudi D/tofa Pyramid Radio… Chiefwip

6- Muhd Mahmud Adam Arewa Radio… Welfare 1

7- Nusaiba Abdul,Aziz Nasara Radio …. Welfare 2

8- Yusif Ali Abdallah Freedom Radio…Pro 1

9- Ibrahim Aminu R/kebe Aminci Radio…. Pro 2

10- Aliyu Wali Dala Radio….. Ex-offico

1 COMMENT

  1. Allah yataya su riko yasanya Alkhairi da albarka.

    Allah ya kara kawowa kano zaman lafiya da kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...