Abun da aka cimma a taron Gwamnonin Arewa maso gabas

Date:

Daga Zara Jamil Isa

GWAMNONIN AREWA MASO GABASHIN NAJERIYA SUN NEMI RUNDUNAR SOJI DA SU RIKE WUTA WAJEN YAKI DA TA’ADDANCI

Gwamnonin yankin arewa maso gabas sun nemi sojoji da su rike wuta wajen yaki da ta’addanci musamman yanzu da aka samu rarrabuwan kawuna tsakanin ‘yan ta’addan.

Gwamnonin sun yi wannan kiran ne a ranar Talata a wajen wani taro da suka gudanar karo na 5 na kungiyar gwamnonin Arewa maso Gabas da aka gudanar a gidan Gwamnatin Jihar Taraba da ke Jalingo.

Sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta fadada aikin binciken mai zuwa Kogin Chadi domin sanya jihohin arewa maso gabas cikin jerin jihohin da ke da arzikin mai.

Dama dai lokaci zuwa lokaci gwamnonin sukan gudanar da irin Wannan taro domin Nemo bakin zaren Matsalolin da suke damun yankin Musamman matsalar tsaro wacce ita ce tafi ci musu tuwo a kwarya.

219 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar...

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...