Harin Yan Bindiga: Shugaban Kasar Niger ya jajantawa Ganduje

Date:

Daga Abubakar Sa’eed Suleman

Shugaban Kasar jamhoriyar Niger Muhd Bazoum ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Kano bisa ga iftila’in hari da yan bindiga Suka kaiwa tawagar gwamnan kano a Lokaci da suke Kan hanyar su ta dawowa daga jihar Zamfara

Muhd Bazoum ya bayyana hakan ne lokaci da ya jagoranci Wata tawaga zuwa Gidan gwamnatin jihar Kano domin yiwa Gwamna Ganduje jaje.

Shugaban Kasar Wanda Gwamnan jihar Damagaran dake jamhoriyar Niger Alhaji Musa Isa ya Wakilta yace abun da ya faru abun takai ci me.

Yace matsalar Tsaro da ta addabi kasashen Nigeria Camaro da Niger jarrabawa ce Daga Allah Kuma yayi fatan Waɗanda Suka Jikkata Allah ya basu lafiya ya kiyaye hakan a nan gaba.

Bazoum yace sun zo Kano ne domin taya Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Murnar bashi Sanda da aka yi a Ranar Asabar din data gabata.

Yace sun yaba sosai da irin Karramawar da aka yi musu kafin taron lokacin taron da bayan taron,Amma yace basu yi mamakin karramawar ba idan akai la’akari da dangantakar dake tsakanin Kano da Niger.

A nasa jawabin Gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa ayari bisa amsa gayyatar da aka yi musu ,Sannan yayi musu fatan kokawa gidan lafiya.

77 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...