Daga Halima Musa Sabaru
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bada umarnin kama duk wanda ya ki karban tsofaffin kudi na naira dari biyu, dari biyar da dubu daya a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jamilu Iliyasu Birnin Magaji, sakataren yada labaran gwamnan jihar ya fitar a ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce Matawalle ya bayyana hakan ne a wajen bikin rantsar da sabbin alkalan babbar kotuna da sabbin masu ba da shawara na musamman da aka nada a gidan gwamnati, dake Gusau, babban birnin jihar.

A cewar sanarwar, shi da takwarorinsa na jihohin Kogi da Kaduna suna neman kotun kolin kasar da ta ba da umarnin tsawaitawa tare da cigaba da amfani tsoffin takardun kudi na naira 200, 500 da 1000.

Gwamna Bello Matawalle ya kuma yabawa kotun koli bisa yin abin da ya kamata, wanda a cewarsa hakan zai rage radadin halin da talakawa su ke ciki.
Ya bayyana farin cikinsa cewa yanzu tsohon kudin ya fara aiki kuma har yanzu mutane na iya amfani dasu a harkokin su na kasuwanci .