Daga Kamal Yakubu Ali
Wani dan kasuwa a nan kano Alh munzali Sani Musa ya bukaci mawadata dake cikin al’umma dasu tallafawa mabukata gwargwadon iko duba da halin matsi da al’umma ke ciki musamman da abinda zasu cigaba da gudanarda da rayuwarsu.
Kadaura24 ta rawaito Alhaji munzali sani Musa ya bayyana hakanne a yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa.
Ya ce yawan sadaka da kyauta baya rage yawan dukiya, sai dai ya kara habbaka ta kamar yadda Allah subhanahu wata Allah ya bayyana a cikin Alkurani mai girma, cewa duk abinda ka bayar zai dawo maka dashi.

“Ku taimakawa al’umma da abun da Allah ya hore muku domin rage musu radadin halin da suke ciki , idan kukayi hakan Allah zaiyi farin ciki da hakan” . Inji Alh. Munzali Sani

Ya kuma Kara da cewar Annabi sallallah Alaihi wasallam yace kayi sadaka koda da barin dabino ne, ka baiwa dan uwanka shi ma. Allah yana farin ciki da hakan.
Yace mutukar mawadata dake jihar nan suka jajirce wajan tallafawa yan uwansu da sauran al’umma dake tare dasu, babu shakka za a sami sauki a halin Kunchi da ake ciki musamman ta hanyar samar musu abincin da sauran bukatun sa na yau da kullum.
Ya bayyana cewa duk wanda Allah ya yalwata masa da dukiya babban abinda zai yi wajan ganin dukiyar nan ta dawwama shi ne tallafawa mubakata ta fannoni da dama, Hakika Allah zai sanya Albarka a wannan dukiya dama zuriarsa baki daya.