Kishin al’umma ne yasa Ganduje ya maka Buhari a Kotu – Musa Iliyasu Kwankwaso

Date:

Daga Nura Abubakar Cele

 

Ɗan takarar majalisar tarayya a wakilcin ƙananan hukumomin Madobi, Kura da Garin Mallam, Hon. Dr. Musa Ilyasu Kwankwaso, ya yabawa gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, na ɗaukar matakin kai gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ƙara kotu dangane da sauya fasalin wasu daga cikin kuɗaɗen Nigeria.

 

Hon. Dr. Musa Ilyasu Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da Kadaura24 a rana ranar Juma’a.

Talla

Musa Iliyasu Kwankwaso wanda shi ne Sarkin yakin Masarautar Karaye, ya ce gwamnan babban bankin ƙasa CBN ya fito da tsarin canjin kuɗin ne Saboda  baƙin cikin rasa takarar shugaban kasa da yayi a jam’iyyar APC.

 

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Musa Ilyasu ya kuma ce kamata yayi sauran gwamnonin Najeriya suma su yi koyi da Gwamnan Kano wajen ɗaukar mataki ga dukkanin waɗanda suke da ruwa da tsaki kan batun sauya wasu nau’o’in kuɗaɗen Naira a ƙasa, da suka haɗar da Naira 1000, 500, da kuma 200.

 

“Kamata yayi duk ƴan Najeriya su fara kai bankunan da suka rufe ƙara a kotu, bisa hanasu kuɗaɗen da suka ajiye a bankuna.” Inji Musa Ilyasu Kwankwaso

Ya kuma ƙalubalanci Alhaji Ahmadu Haruna Dan zago, kan ganin baice gwamna Ganduje da yake yi, akan adawar da gwamnan yake yi da sabon tsarin kudi, Inda yace Dan zago shi ne ya fara kalubalantar Shugaban kasa Muhammadu Buhari” a cewar Musa Iliyasu Kwankwaso

 

Gwamnatin Jihar kano dai ta kai gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kara a gaban Kotun Kolin kasar a kan sauyin fasalin wasu daga cikin manyan kuɗin kasar na Naira 200 da 500 da 1000.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce al’umma sun shiga mawuyacin halin sakamakon wannan tsarin na CBN , to damuwa da yanayin da jama’a suke ciki ne yasa gwamna Ganduje daukar wannan mataki da duk jama’a suke goyon baya.

 

A karar wadda Babban Lauyan jihar ta Kano ya shigar ta hannun Sunusi Musa babban lauya a Najeriya (SAN), a jiya Alhamis, gwamnatin tana bukatar kotun ta ayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari shi kadai ba shi da hurumin umartar Babban Bankin Kasar, CBN ya dakatar da amfani da takardun kudin ba tare da tuntuba da amincewar majalisar tattalin arziki da kuma majalisar zartarwa ta kasar ba.

 

Kazalika a don haka ne ma gwamnatin jihar ta Kano take son Kotun ta soke matakin Babban Bankin na Najeriya na janye takardun kudaden saboda abin ta kira wahalar da al’ummar jihar ke ciki asaboda matakin na CBN.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...