Sheikh Karibullah ya Nada Sabon Mukaddamin Kadiriyya a Unguwar Soron Dinki

Date:

Daga Shehu Sulaiman Sharfadi

 

Shugaban darikar kadiriyya na yammacin kasashen Afrika Sheikh karibullah Nasiru kabara ya ja hankalin mukaddami sabon nuraddin da aka nada Malam Dahiru umar da yayi koyi da halayen mahaifinsa wajen ilmantarwa da kuma dabbaka harkokin addinin musulunci a ma jihar kano da kasa baki daya.

Shek karibullah Nasiru kabara ya yi wannan jan hankalin jim kadan da nada sabon mukaddamin malam Nuraddin Dahiru umar wanda zai rika kulawa da harkokin addinin musulunci a unguwar soron dinki, taron wanda aka gudanar da shi a gidan Kadiriyya dake kano.
Talla
Shugaban darikar na bayyana cewar marigayi malam Dahiru soron dinki fitaccene kuma jajirtaccen malami da kare rayuwar sa wajen hidintawa addinin musulunci, wanda hakan ta sa aka zabo dansa malam Nuraddin Dahiru domin ya zama halifan mahaifin sa, sakamakon shi ma yana da Ilimi da mu’amalar da zai iya rike halifancin mahaifinsa.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
Ya kara da cewar daga cikin ayyukan mukaddami shi ne koyarwa, ilmantarwa da horas da matasa da Sauran al’umma kan gwadaben ambaton Allah da kuma neman yarda da neman kusanci Allah subhanahu wata’ala.
Yayi wa sabon mukaddamin addu’ar samun damar sauke nauyin da ya rayata a wuyansa, tare da yi masa fatan alkhairi da kuma neman gafara da rahama ga mahaifinsa malam Dahiru soron dinki.
A nasa jawabin sabon mukaddamin malam nuraddin Dahiru umar ya bayyana godiyarsa ga Allah subhanahu wata’ala bisa wannan nadin da Khalifa darikar kadiriyya Shek karibullah Nasiru kabara ya yi masa, tare kuma da yiwa mahaifinsa adduar samun rahama a gurin Allah, inda kuma ya roki Allah ya yi riko da hannunsa wajen kwatanta halaye da dabiun mahaifinsa.
Ya kuma yi godiya ga Khalifa darikar kadiriyya bisa wannan amana da aka dora masa, inda kuma ya yi kira jagorori da kuma yan uwansa da aka dora wannan amana da su daure su sauke wannan nauyi da aka dora musu.
Daga karshe yayi al’umma fatan alheri bisa samun dama da suka yi wajen halartar taron kaddamar dashi a matsayin Halifan mahaifinsa tare da bada tabbacin zai yi iya bakin kokarin sa don sauke nauyin da aka dora musa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NNPPn Kano ta bayyana matsayar Kwankwaso kan batun yi wa Tinubu mataimaki a 2027

Shugabanin bangarori biyu na jam’iyyar NNPP a jihar Kano,...

A Gaggauce: Fadar shugaban Kasa ta musanta murabus din Sakataren gwamnatin tarayya

Daga Rahama Umar Kwaru Fadar shugaban Kasa ta musanta labarin...

Gawuna ya mika ta’aziyyar rasuwar Alhaji Aminu Dantata

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna...

Nijeriya ta yi babban rashi: Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Aminu Dantata

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya...