An tsige Limamin wani masallaci da ke unguwar Madina a cikin birnin Bauchi, mai suna Dahiru Abubakar, daga mukaminsa bisa zargin amfani da wa’azi wajen yi wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, kamfen gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Rahotanni sun bayyana cewa limamin ya sha bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Tinubu a lokacin wa’azinsa ga masu ibada bayan kammala sallolin farilla.

Ana zargin matakin tsige shi ya biyo bayan sake maimaita irin wannan magana bayan sallar Asuba a ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ba shi ne ya haddasa matsalar rashin tsaro a Najeriya ba, tare da jaddada cewa ya cancanci samun damar sake jagorantar ƙasar bayan zaɓen 2027.
Dalilin Da Ya Sa Limamin Ke Kare Tinubu
Da yake bayanin dalilin saƙonnin da yake isarwa ga jama’a, Dahiru Abubakar ya ce yana ƙoƙarin wayar da kan al’umma ne domin su daina ɗora wa Shugaba Tinubu alhakin dukkan matsalolin tsaro da ƙuncin tattalin arzikin da ƙasar ke fuskanta.
Ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro ba ta shafi Najeriya kaɗai ba, domin akwai wasu ƙasashen Afirka, ciki har da Sudan, Chadi da Mali, waɗanda su ma ke fuskantar irin waɗannan ƙalubale.
A cewarsa, saƙonnin da yake isarwa ga masu ibada sun fi mayar da hankali kan tsoron Allah, kyautata rayuwar yau da kullum da kuma yin addu’a domin Allah Ya kawo mafita daga matsalolin da ƙasar ke ciki.
Sai dai limamin ya kuma bayyana cewa yana ƙarfafa al’umma su bai wa Tinubu wata dama ta sake jagorantar Najeriya bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Kwamitin Masallaci Ya Bayyana Dalilin Tsige Shi
A nasa ɓangaren, shugaban kwamitin gudanarwar masallacin, Imam Abubakar Jibrin, ya bayyana cewa goyon bayan Tinubu kaɗai ba shi ne dalilin tsige Dahiru Abubakar ba, illa zargin mayar da masallacin wajen gudanar da harkokin siyasa.
Jibrin ya ce kwamitin ya sha gargaɗin limamin kan amfani da masallaci wajen tattauna siyasa da kuma tara jama’a domin gudanar da ayyukan siyasa.
Ya jaddada cewa duk da muhimmancin siyasa wajen zaɓen shugabannin ƙasa, bai kamata a mayar da masallatai wuraren gudanar da kamfen ko tarukan siyasa ba.
A cewarsa, ofisoshin jam’iyyun siyasa da sauran wuraren da suka dace ne ya kamata a gudanar da irin waɗannan ayyuka, ba cikin masallatai ba.
Rikici Kan Sauya Sunan Masallaci
Baya ga batun siyasa, shugaban kwamitin ya kuma zargi Dahiru Abubakar da dagewa kan sauya sunan masallacin daga Masjid Abdullahi Bin Zubbair zuwa Masjid Imam Bola Ahmed Tinubu.
Jibrin ya bayyana cewa kwamitin ya ƙi amincewa da wannan buƙata, bisa hujjar cewa masallacin mallakin al’umma ne, don haka ba mutum ɗaya ne zai sauya masa suna bisa ra’ayinsa ba.
Ya ce kwamitin ya yanke shawarar ci gaba da amfani da sunan masallacin na asali, tare da tabbatar da cewa ba za a mayar da Abubakar kan mukaminsa na limanci ba.
Read also: Malam Shekarau Ya Yiwa Abba da Gawuna Nasiha Kan Hukunci Kotun Ƙoli
Read also: Yanzu-Yanzu :Tawagar jami’an tsaro sun fatattaki wasu Yan Bindiga a Katsina

Ba Adawa Da Tinubu Ko Wani Ɗan Siyasa Ake Yi Ba — Kwamitin
Shugaban kwamitin ya ƙara da cewa shi da sauran mambobin kwamitin ba sa adawa da Shugaba Tinubu ko wani ɗan takarar siyasa.
Sai dai ya ce matsayinsu shi ne, ya kamata masallaci ya kasance wurin bautar Allah, gudanar da ibada da kuma koyar da addini, ba wajen gudanar da harkokin siyasa ba.
Ya bayyana cewa abin da suke fata shi ne al’umma su mayar da hankali wajen roƙon Allah Ya zaɓa musu shugaba nagari wanda zai zama alheri ga Najeriya, ba tare da la’akari da wanda zai tsaya takarar shugabancin ƙasar ba.